Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Tsaro A Sudan Ta Kudu Ya Nakasa Taro Kan Makamashi


Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir

Maitar son mai bai sa manyan kamfanonin mai na duniya sun rufe ido sun halarci wani babban taron da aka shirya masu game da man fetur ba a Sudan Ta Kudu, inda tashin hankali ke neman zama al'amarin yau da kullum.

Kodayake gwamnatin Sudan Ta Kudu ta ce harkokin kasuwanci sun yi cikakken dawowa a kasar, ba a ga Shugaban kasar ba a babban taron da ta kira a karo na farko kan makamashi, wanda ya samu halartar wasu manyan kamfanonin mai kalilan kawai.

Kwararru kan mai sun ce kasar Sudan Ta Kudun ta na da gangar mai wajen biliyan uku da rabi da ba a ma taba ba, baya ga iskar gas mai yawan tukunyar Meter biliyan 85, wadanda ya kamata manyan kamfanonin mai su yi kwadayinsu.

To saidai kuma Sudan Ta Kudun na fama da mummunan tashin hankali wanda ke shiga shekara ta hudu. Mutane miliyan hudu - wanda kusan 1/3 na yawan al'ummar kasar kenan - sun rasa muhallansu, a yayin da kimanin miliyan biyu su ka gudu zuwa kasashen ketare.

Duk kuwa da irin kalubalen da ke tattare da duk wani yinkuri na saka jari a Sudan Ta Kudun, Mataimakin Shugaban Kasar, James Wani Igga, wanda ya wakilci Shugaban kasa Salva Kiir, ya ce Sudan Ta Kudu za ta zama wata babbar kasar mai tasiri, mai mashahurin bangaren man fetur.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG