Accessibility links

Rigakafin Polio Bai Bambanta Da Na Sauran Cututtuka Ba

  • Garba Suleiman

Shugabannin al'umma, ma'aikatan lafiya, malaman addinin Islama da masu fama da Polio su na aikin rigakafi ga yara a Najeriya

Dr. Lawal Aliyu Rabe, yayi bayanin yadda aka gano magungunan rigakafi, da kuma yadda ake harhada su, musamman na Polio, domin kare yara daga zamowa guragu

A shekarun baya, wani likita ya lura da cewa duk matan da suke aikin tatsar nonon shanu, ba su kamuwa da cutar agana, kamar yadda sauran jama'a ke kamuwa. Don haka, sai yayi bincike, sai ya gano cewa su ma shanun su na dauke da wata kwayar cutar agana irin tasu, amma ba ta illa ga dan Adam.

Matan sun kamu da wancan agana ta shanu, ba ta yi musu illa ba, kuma idan ta dan Adam ta shiga jikinsu sai ta mutu, ita ma ba ta iya musu illa. Ashe kwayoyin halittar kare jikinsu ne, suka lakanci yadda zasu iya yakar kwayar cutar agana, ta yadda ko ta dan Adam din tazo, ita ma su na iya murkushe ta. Ta haka, aka gano rigakafin cutar agana, wadda a yau an shafe ta daga doron kasa, babu ita kuma.

Dr. Lawal Aliyu Rabe, darektan Hukumar Kiwon Lafiya tun daga tushe a Jihar Katsina, shi ne yayi wannan bayanin a lokacin da yake musanta jita-jitar da wasu ke bazawa cewa wai maganin rigakafin cutar Polio da ake ba yara, kwayoyin cutar ce ake saka musu.

A wurin taro da VOA Hausa ya shirya a Katsina, kwararren likitan yace ai da ma nau'o'i biyu ake da su na maganin rigakafin kowace irin cuta a duniya: Nau'in farko shi ne na yin amfani da ainihin kwayar cutar wadda aka cire abinda ke cutar da jama'a daga jikinta, ko kuma a samo abinda ke cutar da jama'a daga jikinta, a kashe kaifinsa ta yadda ba zai cutar ba, sannan a sanya ma mutum.

Makasudin bin wadannan hanyoyi kuwa, shi ne kwayoyin halittar kare jiki, wadanda Allah Ya halicci kowa da su a cikin jikinsa, zasu nazarci wadannan kwayoyin cuta ko kuma irin cutar ta su, su samo hanyar kashe ta, ta yadda a duk lokacin da wannan cuta ta zahiri ta zo shiga jikin mutum, to da ma kwayar halittar kare jikinsa sun riga sun tanadi makaman da zasu iya yakar wannan cuta da su.

Ga cikakken bayani daga bakin Kwararren Likitar...
XS
SM
MD
LG