Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigimar Shahararren Mai Sarrafa Fina-finai a Amurka Harvey Weinstein Bata Kare Ba


Harvey Weinstein shahararren mai sarrafa fina-finai
Harvey Weinstein shahararren mai sarrafa fina-finai

Har yanzu rigima na nan tafe ga shaharerren mai sarrafa fina-finan nan na Amurka mai suna Harvey Weinstein, wanda asirinsa ya tonu kwanan nan.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fadi jiya Lahadi cewa ya fara daukar matakin janye lambar girma ta Faransa mai suna "Legion of Honor" da aka taba baiwa Weinstein, wadda itace karramawa mafi daraja a kasar Faransa kuma daya daga cikin lambobin yabo mafiya dajara a duniya.

A shekarar 2012 ce kasar Faransa ta baiwa Weinstein wannan lambar yabon saboda rawar da ya taka wajen yada silima din Faransa da na sauran kasashen Turai a duniya.

Wasu 'yan wasan kwaikwayon Faransa hudu na daga cikin mata 13 da ke zargin Weinstein da aikata batsa da kuma kokarin yin lalata da su cikin tsawon shekaru gommai da su ka gabata.

Wannan babbar cikas da Weinstein ya samu, ya zo ne kwana guda bayan da Cibiyar Fasaha da Kimiyyar Hotunan Majigi ta Amurka, ta kada kuri'ar gaggauta cire Weinstein.

A makon jiya ita ma cibiyar Silima din Burtaniya ta dakatar da Weinstein.

Hatta kwamitin gudanarwar kamfanin Weinstein, mai suna Weinstein Co., ya kore shi, bayan wani rahoton jaridar New York Time mai cike da abin fallasa, inda mata wajen 13 din su ke zarginsa da aikata batsa da kuma neman yin lalata da su

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG