Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigingimun Boko Haram Sun Rutsa da Gidaje Kimanin Miliyan Daya a Jihar Borno


Arch. Yerima Saleh, babban sakataren ma'aikatar sake gine-gine, sake farfado da wuraren jin dadi da sake tsugunar da al'umma ta jihar Borno
Arch. Yerima Saleh, babban sakataren ma'aikatar sake gine-gine, sake farfado da wuraren jin dadi da sake tsugunar da al'umma ta jihar Borno

Yayinda yake jawabi ga manema labarai Yerima Saleh ya ce kimanin gidaje miliyan daya ne da suka hada da makarantu da asibitoci da rijiyoyin burtsatsai mayakan Boko Haram suka lalata ko suka kone a kananan hukumomi 22 cikin 27 dake jihar ta Borno.

Gwamnatin jihar Borno tace kimanin gidaje miliyan daya ne aka kona ko aka lalata sakamakon rigingimun 'yan kungiyar Boko Haram da ya shafi kananan hukumomi 22 cikin 27 dake jihar.

Babban sakataren ma'aikatar sake gina gidajen da rigingimun ya rutsa dasu Arch. Yerima Saleh ya bayyanawa manema labarai a garin Maiduguri. Gwamnati ta samu wannan kidigdigan ne sakamakon wani rahoton hadin gwuiwa tsakanin gwamnatin da wasu kungiyoyi masu zaman kansu.

Shi rahoton an fitar dashi ne a watan Fabrairun shekarar 2015 wanda ya bayyana cewa gidajen, walau an konasu ko an lalatasu. Yanzu yawan gidajen da rikicin ya rutsa dasu sun fi miliyan daya saboda lokacin da aka fitar da rahoton ba'a iya kai wasu wurare ba domin dalilan tsaro, inji Arch. Yerima Saleh.

Cikin gidaje da gine ginen da 'yan ta'addan suka lalata ko suka konesu sun hada da azuzuwan karatu fiye da dubu biyar na makarantu. Asibitoci ko dakunan shan magani sun fi dari biyu da 'yan ta'addan suka lalata. Rijiyoyin burtsatsai fiye da dubu biyu suka salwanta. Rijiyoyin gargajiya kuwa cikasu aka yi da gawarwakin mutane.

Yanzu gwamnatin jihar Borno ta fara aiki a kananan hukumomi 14 cikin 22 da aka kwato daga hannun 'yan Boko Haram din.

Rahoton na shekarar 2015 da aka fitar na nuni da cewa barnar da Boko Haram ta yi a jihohin arewa maso gabas sun fi na dalar Amurka biliyan shida. Kashi biyu cikin uku na barnar da 'yan ta'addan suka yi sun yi ne a jiahr Borno saboda hatta hanyoyi basu tsira ba a jihar. Misali, Arch. Yerima Saleh yace tsakanin Pulka da Gwozah tazarar kilomita ishirin ne kawai amma sai da suka yi awa hudu a mota kafin su kai Gwozan daga Pulka bayan sojoji sun sha jire nakiyoyin da 'yan ta'addan suka dasa.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG