Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nemi da a kai zuciya nesa a rikicin da ke faruwa tsakanin al’umar Jukun da Tiv a jihar Taraba da kuma wanda ke faruwa a Adamawa tsakanin Fulani, Gejon da Bachama.
Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, wacce Muryar Amurka ta samu, inda ya nuna alhininsa dangane da wadannan rikice-rikice da ke faruwa.
“Tashin hankali da zubar da jini, ba zai amfani kowa ba, kuma abu ne da ba za mu lamunta ba, muna kuma Allah wadai da su, musamman a daidai wannan lokaci da ake bukuwan Easter.”
Buhari ya kara da cewa, kamar yadda sanarwa ta nuna, “tashin hankali ba shi ne maslaha ga rashin jituwa da muke samu a tsakaninmu.”
Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Buhari ya umurci wata kungiyar addini, wacce ta yi nasarar dinke rashin fahimtar da ke tsakanin al’umomi daban-daban a jihar Pilato, da ta yi aiki da hukumomin tsaro domin sasanta rikicin Kaduna, Taraba da Adamawa.
Sannan ya umurci, hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA da hukumar kula da ‘yan gudun hijira, da su dukufa wajen tallafawa wadanda rikicin ya shafa.
Ya kuma ce, tuni dakarun kasar suka yi nasarar, maido da zaman lafiya a tsakanin al’umomin wadannan yankuna.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 05, 2023
Yajin Aiki: Tinubu Zai Kafa Kwamiti Don Duba Bukatun NLC
-
Yuni 04, 2023
Kaura Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP
-
Yuni 03, 2023
Ana Ci Gaba Da Takaddama Kan Cire Tallafin Man Fetur