Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Kabilanci Ya Rutsa da Akalla Mutane 24 A Dimokradiyar Kongo


Shugaban Dimokradiyar Kongo Joseph Kabila
Shugaban Dimokradiyar Kongo Joseph Kabila

Barkewar rikicin kabilanci tsakanin kabilun Hema da Lendu a arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Konko ya rutsa da mutane fiye da 24 lamarin da rundunar samar da zaman lafiya ta MDD ta ce zata bincika

Barkewar wani rikicin kabilanci a Arewa maso gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo, ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da 24, da kuma kona daruruwan gidaje kurmus.

Jami’an kasar Congo, sun bayyana cewa rikicin ya barke ne a satin da ya gabata a lardin Ituri tsakanin ‘yan kabilar Hema da ‘yan kabilar Lendu.

Babu tabbacin abinda ya haifar da rikicin, amma an san cewa kungiyoyin biyu sun dade suna gaba mai tsanani da junansu.

Rundunar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, a Kongo din, ta ce zata yi binciki akan lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG