Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Makiyaya da Manoma a Yola Ya Rutsa da Rayyuka Shida


Gwamnan Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
Gwamnan Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Mutane shida da suka hada da jami’an tsaro suka rasa rayukansu sanadiyar rikincin da ya barke tsakanin Fulani makiyaya da manoma a karamar hukumar Yola ta Kudu cikin jihar Adamawa

Kawo yanzu dai mutane shida ne rahotanni suka bayyana cewa sun mutu ciki kuwa harda jami’in dan sanda, da yan banga biyu a wani rikici da ya barke a tsakanin Fulani makiyaya da kuma wasu manoma a cikin karamar hukumar Yola ta kudu dake tsakiyar jihar Adamawan.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, yace shi da kansa ya ga gawar dan sanda dayan da aka kashe.

To sai dai yayin hada hancin wannan rahoto, Kakakin rundunan ‘yan sandan jihar SP Othman Abubakar yace mutum guda ne aka kashe, yayin da aka baza jami’anta don cafko mabarnatan.

Haka shima dai da yake karin haske, kakakin rundunan jami’an tsaron farin kaya ta sa-kai,Suleiman Baba ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG