Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Shugabanci Na Kokarin Raba Kawunan ‘Yan Jam’iyyar APC A Adamawa


Jihar Adamawa

Rikicin shugabanci da ya kunno a Jam’iyyar APC dake mulki jihar Adamawa na daukar sabon salo, lamarin da ya kai wasu ya yan Jam’iyyar yin fatali da matakin da uwar jam’iyya ta kasa ta dauka na nada yan kwamitin riko karkashin jagorancin shugaban Jam’iyyar na karamar hukumar Michika Hon Ibrahim Bilal.

Wasu yan jam’iyyar kuma na zargin cewar da hannun sakataren gwamnatin tarayya Mr Bidi Lawal, a wannan rikicin, batun da suka ce bazasu amince ba, su kuwa ‘yan ‘daya bangaren na musunta wannan zargi.

Hon Usaini Gambo Bello, dake zama shugaban yan shinkafa na Jam’iyyar yace bazata sabu ba bindiga a ruwa, yakuma zargi wasu manyan da suke sama da cewar sune ke lalata lamarin, domin wasu na da kishin jihar Adamawa, wasu kuwa basu da shi.

Shugaban rikon kwamitin da aka kafa Hon Ibrahim Bilal, ya musunta wannan zargi inda yace sun zone domin suyi gyara.

Amma wasu yan Jam’iyyar sun fara gargadin gwamnan jihar Sanata Bindo Umaru Jibrilla, da ya tsome hannunsa a wannan rikici da ke faruwa yanzu a jihar.

Yanzu haka dai lokaci ne kan iya tabbatarwa da yadda zata kasance yayin da iyalan gidan siyasar Murtala Nyako ke kada gangan zuwa kotin koli.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG