Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Sojoji Da Direbobin Manyan Motoci Ya Gurgunta Hanyar Apapa, Lagos


Wasu sojoji a Apapa, Lagos

Yayin da Najeriya ke kara azama a yaki da cin hanci da rashawa, wani kazamin rikici ya barke tsakanin sojoji da direban motoci kan abin da aka ce na da nasaba da karbar na goro

Wata rigimar da ta kunno kai tsakanin sojoji da direbobin manyan motoci ta janyo cunkushewar hanyar zuwa tashar jirgin ruwa ta Apapa, Lagos.

Direbobin na zargin sojojin ne da yawan karbar na goro, al’amarin da ya kai ga takaddama tsakanin wani direba da yaron mota a gefe guda da kuma sojoji a daya bangaren a daren jiya, wanda ya kai ga dokar kawo wukar da aka yi ma yaron motar, wanda a yanzu haka ya na asibiti rai ga hannun Allah.

Direban mai suna Ayuba Abdullahi ya shaida ma wakilinmu a Lagos Babangida Jibrin cewa sojojin sun tsai da shi ne a kan hanyarsa ta zuwa wurin lodi, sai ya bai wa mai karba masu na goro Naira 200, sai wani soja ya ruga ya kama miron motarsa y ace ai Naira 1000 ake bayarwa ba 200 ba. Sai ya umurce shi ya tsaya sai ya tsaya, sai wani ya harba bindiga ya umurce su da su sauko su ka ki, sai su ka farfasa gilashin motar. Da babban nasu shi ma ya zo sai ya umurce shi da ya yi ta jujjuyawa a wurin shi kuma yaron mota aka kwade shi da wani katako har ya suma.

Shi ma wani shugaban kungiyar direbobin mai suna Kwamrad Musa Shagiri, ya tabbatar da lamarin, amma y ace ba za a iya bude hanyar ba har sai direbobin sun yanke shawarar yin haka kuma sojojin sun amince su biya barnar da su ka yi. Y ace kungiyar direbobin ce ma ta dauki nauyin jinyar yaron motar ba sojojin ba.

To sai dai wakilnmu Babangida Jibrin, y ace duk kokarinsa na jin ta bakin sojojin ya ci tura saboda hatta kwamandan sojojin na yankin na Apapa ya ce shi ba zai yi magana ba.

Ga Babangida da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG