Mutanen da suka rasa gidajensu sanadiyar hare-hare da mutanen Tarok suka kai masu suna cikin wani halin lahaula walakawati. An kone gidanjensu kana su da yaransu suna nan kara zube a wasu makarantu firamari inda ba wuta ba ruwa sai sauro da suka dira kansu.
Hukumomin Taraba sun tabbatar da cewa muatane fiye da dubu uku suke gudun hijira banda wadanda suka bace domin ba'a san inda suke ba. Sun ce gwamnati na iyakacin kokarinta ta taimaki mutanen.
Ibrahim Abdulaziz nada rahoto.