Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikita-Rikita A Majalisar Wakilan Najeriya


Majalisun Dokokin Najeriya

Wanene ke da hurumin sake kiran zaman Majalisar Wakilan Najeriya daga hutun da ta ke yi?

'Yan Majalisar Wakilan Najeriya na ci gaba da furta albarkacin bakin su a daidai lokacin da mai shari'a Ahmed Ramat Mohammed ya yanke hukuncin cewa Shugaba Goodluck Jonathan da jam'iyar PDP mai mulki su dakatar da batun sake kiran zaman Majalisar wakilai daga hutu. 'Yan majalisar wakilan Najeriya sun ce ko da ma ba a kai maganar kotu ba, babu dokar da ta baiwa shugaban kasa da jam'iyar sa ta PDP hurumin kiran zaman majalisar. Madina Dauda ta hada rahoto akan wannan sabuwar badakala da ta kunno kai a majalisar wakilan ta kasar Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

Wannan badakala dai na da nasaba da canjin shekar da kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Barista Aminu Waziri Tambuwal yayi daga Jam’iyyar PDP mai mulki zuwa Jam’iyyar adawa ta APC.

XS
SM
MD
LG