Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Robert Mueller Ya Kusa Kammala Bincikensa - Whitaker

MUkaddashin Atoni Janar na Amurka Matthew Whitaker

Ya kara da cewa, “Yanzu haka, wannan binciken, a gani na, na dab da kammala, kuma ina fatan za mu samu rahoton daga Mueller ba tare da bata lokaci ba.”

Binciken zargin katsalandan din Rasha a zaben Amurka na 2016, wanda mai bincike na musamman, Robert Mueller ke jagoranta, na gab da kawowa karshe.

Mukaddashin Attoni-Janar din Amurka Matthew Whitaker ne fadawa manema labarai jiya Litinin.

Ya kara da cewa, “Yanzu haka, wannan binciken, a gani na, na dab da kammala, kuma ina fatan za mu samu rahoton daga Mueller ba tare da bata lokaci ba.”

A baya-bayan nan binciken ya kai ga damke wani dadadden aminin Shugaba Donald Trump mai suna Roger Stone, kuma ya kai ga samun tsohon manajan kwamitin yakin neman zaben Trump Paul Manafort.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG