Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Roger Moore Ya Mutu Yana Da Shekaru 89 a Duniya


Britain Roger Moore Obit

Sanannan 'dan wasan kwaikwayon siniman nan, 'dan kasar Birtaniya Roger Moore, wanda akafi sani cikin fina-finan da yayi a matsayin James Bond, ya mutu yana da shekaru 89.

A wata sanarwa da ‘ya ‘yan marigayin suka fitar jiya sunce “cikin bacin rai muke bada sanarwar mutuwar mahaifinmu, Roger Moore, ya mutu a kasar Switzerland, bayan wata ‘yar fama da cutar daji da yayi.”

Za ayi jana’izarsa ne a Manaco, kamar yadda ya bada wasiya a cewar ‘ya ‘yan nasa.

Moore, yana daga cikin dadaddun jakadun taimako na asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya da ake kira UNICEF, inda ya ziyarci shirye-shiryen da aka tsara domin inganta rayuwar yara a kasashe sama da 16. Ya kuma samu lambar yabo ta Lifetime achievement award a shekara ta 2012.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Yadda Aka Yi Na Samu Mabiya Miliyan Daya a Shafina Na Instagram - Daso
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG