Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rohingya: Indonesia Ta Tura Jami'arta Zuwa Myanmar


Zangar zangar lumana da al'umar Indonesia suka yi a Indonesia domin a kawo karshen rikicin Myanmar

Ministar harkokin kasar waje ta Indonesia, Retno Marsudi, tana ziyara a kasar Myanmar domin ganawa da jagabar al’ummar kasar Aung San Su Kyi, da kwamandan rundunar sojan kasar, da kuma  babban mai  baiwa  shugaban kasar  shawara a harkokin tsaro.

Kasar Indonesia ta tura wata babbar jami'arta zuwa kasar Myanmar domin shiga tsakani a rikicin 'yan kabilar Rohingya da hukumomin jihar Rakhine.

Maksudin ziyarar ita ce domin su tattauna akan abinda ke faruwa a jihar Rakhine.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ’yan asalin jinsin Rohingya su dubu 87 ne suka gudu daga jihar zuwa makwabciyar kasar Bangaladesh tun lokacin da fada ya barke a farkon watan jiya.

Shugaban kasar na Indonesia Joko Wododo, ya ce Ministan tashi za ta bukaci gwamnatin kasar ta Burma da ta hana ci gaba da fadan da ke dalilin kashe mutane, kana daga nan kuma ta zarce zuwa kasar Bangaladesh domin tsara yadda za a taimakawa wadanda suka tsere suka shiga cikin kasar.

Fada na baya-bayan nan shine wanda aka fara a ranar 25 ga watan Agusta, sa'ilin da wasu ‘yan tsagerun Rohingya suka farma wani caji ofis da ma wani sansanin soja a kokarin su na kare ‘yan kabilarsu daga cin zarafin da ake musu.

Rundunar sojan kasar ta ce mutane 400 ne suka mutu yawancin su ‘yan tawaye ne.

Dama dai gwamnatin ta Myanmar tana daukar yan kabilar ta Rohingya a matsayin bakin haure ne daga kasar Bangaladesh, wadanda ba a taba basu takardan iznin zama ‘yan kasa ba duk da yake suna da iyaye da kakanninsu zaune a kasar shekara da shekaru.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG