Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rufe Filin Jiragen Sama Na Abuja da Za'a Yi Ya Jawo Cecekuce


Filin Jiragen Sama
Filin Jiragen Sama

Bayan da gwamnatin Najeriya ta bada sanarwar zata rufe filin jiragen sama na Abuja har na tsawon makonni shida domin a yi masa gyara a kuma karkata akalar masu tafiya zuwa filin Kaduna wasu 'yan kasar sun soma cecekuce akan shirin.

Yawancin masu cecekucen suna ganin a daidai wannan lokacin za'a karawa matafiya wahaloli ne kawai.

Saidai ministan sufurin jiragen sama na Najeriya yayi karin haske akan wannan shirin na rufe filin na tsawon makonni shida kawai.

Ministan Alhaji Hadi Sirika yace gyaran tilas ne a yishi domin a kaucewa hadari. Daben da aka yi na saukan jiragen an yishi ne ya kai shekaru 25 bayan nan a sake yin wani. Yace a birni irin Abuja ya kamata a ce akwai daben biyu.

Lokacin da aka gina filin ana sa zato fasinjoji ba zasu wuce dubu dari ba a shekara amma bayan gwamnatin tarayya ta dawo Abuja yanzu ana samun mutane miliyan takwas kowace shekara. Sauka da tashi suka karu biye da tsammani.

Yanzu daben ya kai shekaru 35 mai makon 25, wato ya kara shekaru goma, wanda ya wuce lokacin da yakamata a sake ginashi. Dalili ke nan da ya sa yana ballewa ana samun ramuka a tsakitarshi.

Wani matukin jirgin sama kuma kwararre a harkokin jiragen sama yace babu makawa tilas ne gwamnati ta dauki wannan matakin.

Ga rahoton Umar Faaruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG