Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rugujewar Gini Ta Hallaka Mutane 10 Tare Da Jikkata Wasu Da Dama A Oyo


Ibadan
Ibadan

Haka kuma an yi nasarar ceto mutane 7 da suka samu nau’ukan raunuka daban-daban daga wurin da al’amarin ya faru a yau Alhamis.

An zakulo gawawwaki 10 daga karkashin baraguzan wani bene daya ruguje a unguwar Jegede da shiyar Olunloyo ta birnin Ibadan, fadar gwamnatin jihar Oyo.

Haka kuma an yi nasarar ceto mutane 7 da suka samu nau’ukan raunuka daban-daban daga wurin da al’amarin ya faru a yau Alhamis.

Sanarwar da janar manajan hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Yemi Akinyinka ya fitar, tace hukumar ta samu kiran gaggawa daga mazauna yankin da misalin karfe 2 da dare cewa wani gini ya rushe tare da danne mutane a karkashin baraguzansa.

Ita ma sanarwar da hukumomin ‘yan sanda suka fitar ta tabbatar da afkuwar lamarin. “An dauki kwararan matakan tsaro a yankin domin hana batagari mamaye wurin da ginin ya rushe sannan ana tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin sauran mazauna yankin,” a cewar ‘yan sanda.

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG