Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar bada kariya Ta Cafke Mutane Matasa 20


 Ibrahim Abdullahi, shugaban Civil Defense
Ibrahim Abdullahi, shugaban Civil Defense

Mutanen da Civil Defense ko rundunar ba da kariya ta kama a jihar Borno ana zarginsu da laifuka daban daban da suka hada da karkata abincin ‘yan gudun hijira da sace kayan hada ruwan famfo da dabbobi kamar akuya tare da bin matan aure suna yaudararsu suna kwace masu wayoyin hannu.

Wasu matasa da suka kirkiro da sabbin salon yin sata a jihar Bornon sun shiga hannun Civil Defense. Kawo yanzu matasa 20 ne rundunar ba da kariya ta nuna wa manema labarai a zaman wadanda aka kama da laifuka.

Shugaban rundunar, Ibrahim Abdullahi, shi ya gabatar da mutanengaban manema labarai a garin Maiduguri. Cikin mutanen har da masu karkata abincin ‘yan gudun hijira. Akwai wasu dake sayar da katin jabu a sansanonin ‘yan gudun hijira. Akwai masu satar awakai. Wasunsu kuma suna hada baki da ma’aikatar samar da ruwa ta jihar Borno suna sace kayyayakin samar da ruwan.

A wani sabon salo kuma da matasan suka bullo dashi su kan yi cefane su kai gidan wasu mutane su ce an aikosu ne. Idan sun ba da cefanen sai su ce maigidan ya gaya masu su karbo wasu kayayyaki. Suna kuma iya kwace wayar uwargidan su ruga da gudu.

Da bakin su matasan suka amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.

Ibrahim Abdullahi shugaban hukumar ba da kariya ya ce matasan basu kyauta ba saboda ko a kayan abinci matasan sun sace buhuna dari biyu na dawa.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG