Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Isra'ila ta Yi Ikirarin Lalata Gidajen Hamas Biyu A Arewacin Gaza


Isreal Palestine
Isreal Palestine

Sojojin Isra’ila sun ci gaba da barin wuta a Gaza babu kakkautawa, inda ta kai harin bama bamai da tanka a kan garin Khan Younis. Rahotanni sun ce wannan fatattakar na zuwa ne gabanin yanda ake zaton zai faru tun farko a cikin garin.

Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP yace daya daga cikin 'ma'aikatan sa yace an cigaba da lugudan wuta a Khan Younis da Rafah. Rafah dai yana kusa da kasar Misra kuma inda dubban Falasdinawa ‘yan gudun hijira suka nemi mafaka daga yakin.

A tsakiyar Gaza, Isra’ila ta kai hare haren sama a kan sansanin Nuseirat.

Ma’aikatar sojan Isra’ila ta ce ta lalata gidajen Hamas biyu a Beit Lahia a arewacin Gaza.

Rahotanni sun ce kashe kashe a Gaza ya biyo bayan da jami’an lafiya a Gaza suka ce an kashe kusan mutane 200 a cikin sa’o’I 24.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana fargaba a kan abin da suka ayyana shi da yunkurin auna ayarin ma’aikatan jin kai da sojoji Isra’ila suke yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG