Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojan Najeriya Ta Kubutar Da Mutane Sama da Dubu 30 Daga Hanun Boko HaramCikin Shekaru 2.


Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara
Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ranar Soja A Zamfara

Rundunar sojan Najeriya tace duk da cewa bata kwato daukacin 'yan matan chibok ba, duk da haka ta sami nasarar kubutar da mutane sama da dubu 30 daga hannun 'yan Boko Haram.

Rundunar Sojan Najeriya Ta Amince Ta Gaza Kwato Daukacin ‘Yan Matan Chibok

Rundunar sojan Najeriya mai kula da yaki da kungiyar Boko Haram tace daga shekaru biyu da suka gabata lokacin kawo yanzu ta samu nasarar kwato mutane 30,000 daga hannun ‘yan kungiyar boko haram.

Da Yake maganada da Muryar Amurka, Ministan tsaron Najeriya,Janar Mansur Dan Ali mai ritaya yace sojoji sun taka rawar gani wajen murkushe kungiyar ta boko haram.

Ministan yace yanzu haka ba wani yanki dake karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram sabaninabinda ke faruwa da.

Shima da yake tsokaci game da wannan yakin da suke yi da ‘yan kungiyar ta Boko Haram, shugaban rundunar sojojin dake wannan aiki, Manjo janar Rogers Ibe Nicholas, yace yanzu haka sunyi nasarar karbe babban hedikwatar ta kungiyar boko haram dake cikn dajin Sambisa.

Yace duk da yake basu samu nasarar kwato daukacin ‘yan matan chibok ba da kungiyar ta sace yau sama da shekaru 4,duk da haka dai tayi nasarar kwato farar hular da ‘yan kungiyar suka kame suka tilasta su zama cikin su.

Jami'an gwamnatin Najeriyan biyu, sun shaidawa wakilin gidan Radiyon nan na Muryar Amurka James Butty cewa, sojoji Najeriya ba zasu yi kasa a gwiwa ba har sai sun tabbatar ba sauran ya’yan wannan kungiyar.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG