Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Najeriya Ta Kwace Garin Dikwa


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri, Mayu 14, 2015.

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa, ta samu nasarar sake kwace garin Dikwa. A cikin hirarsu da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u, mataimakin darektan hulda da jama’a na runduna ta bakwai a Maiduguri, Kanar Tukur Gusau yace ,sun lalata motoci tare da samun makamai masu dama a wurin.

Yace sun sami makaman harbo jirgin sama da albarusansu. Daga ciki, akwai kuma wata bindiga ta musamman da ake kira “General Purpose Machine Gun”, banda haka kuma, yace akwai wata bindiga da mafiya yawa masu amfani da ita, sune sojojin sama, da bindigogi masu sarrafa kansu kala kala.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma sami wayar salula da kuma SIM card guda uku wadanda za a bincika domin neman samun bayanai a cikinsu. Wakazalika rundunar sojin ta samo akwatuna na harsasai na musamman. Bisa ga bayaninsa, an lalata wadansu makaman a can saboda haka ba zasu dauku ba.

Kanar Tukur ya bayyana cewa babu wanda suka kama a samamen sai wadanda suka kashe, yayinda a nasu bangaren ba a kashe kowa ko raunata wani soja ba. Ya bayyana cewa, wannan ne karon farko da sojojin Najeriya suka shiga Dikwa.

Bisa ga cewar Kanar Tukur, a saninsu, babu ko karamar hukuma daya dake hannun kungiyar Boko Haram. Sai dai sun san cewa, wani lokaci sukan shigo suyi barna su saci kayan mutane, amma babu ko Karanar hukuma daya da za a ce gaba daya, wata karama tana hannun Boko Haram.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana

Rahoton Kwace Dikwa-2:51"
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG