Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Runduar Sojin Najeriya Zata Yi Gwajin Makamai A Dajin Sambisa


Shugaban sashin horaswa na rundunar sojin Najeriya Manjo Janar Dede Ahmadu, ya ce gasar harbe harbe ta wannan shekarar ta musamman ce wadda za a gudanar a dajin Sambisa, inda sojin kasar zasu gwada karfinsu, za a kuma yi gwajin barin wuta, makaman yaki na sojin kasa da kuma bindigogin atilare.

Daraktan labarai na shalkwatar sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, ya yiwa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Hassan Maina Kaina, Karin bayanin cewa rawar dajin da jami’am ke yi bayan kowace shekara domin tabbatar da kwarewar aiki, an kwashe kusan shekaru goma ba a yi ba,

Ta dalilin haka ne shugaban rundunar sojin kasar Janar Tukur Buratai, ya umurci jami’an su gudanar da wannan gwaji a dajin Sambisa, kuma za a yi gwajinne ta hanyar fafatawa Tsakanin rundunonin soji, domin inganta kwarewa wajan sanin makamar aiki da amfani da kanana da manyan makamai.

Da yake amsa tambayar da wakilin sashi Hausa, ya yi masa, Kuka sheka, ya bayyana cewa saboda matakan tsaro, da kuma yaki da ake da ‘yan kungiyar boko haram, baza su bari sai ta kwana ba duk da cewa an ci karfin kungiyar, ya kuma kara da cewa a yanzu haka akwai kimamin rundunoni bakwai dake jibge a wannan yanki da ke fama da rikicin boko haram.

Daga Abuja, ga rahoton Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG