Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Tsaron STF Ta Kame Mutum 20 Da Ake Zargi Da Ta’addanci a Jihar Pilato


Rundunar Tsaron STF Ta Kama Masu Aikata Ta'addanci
Rundunar Tsaron STF Ta Kama Masu Aikata Ta'addanci

Rundunar tsaro ta musamman STF a jihar Pilato, ta kame mutane ashirin, da ta ke zargi da aikata manyan laifuka ciki har da kai hari a kauyen Kulben, karamar hukumar Mangu wanda da ya yi sanadiyyar rasa rayuka goma sha biyu a kwanakin baya.

Kwamandan rundunar STF a jahar Pilato, manjo janar Augustine Agundu ya ce, wadanda suka kaman, sun hada da yan fashi da makami da barayin shanu da masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma yan kungiyar asirim sai kuma wani da suke zargi dan kungiyar Boko Haram ne.

Augustine Agundu ya ce jami’ansa sun kame Ya’u Mohammed babban dan fashi da makami a garin Toro, jihar Bauchi in da shi da tawagarsa su ka yi kwantan bauna wa sojoji suka harbe daya daga cikin sojojin a yankin Riyum.

Ya kara da cewa rundunar sun kuma kame wani Ishaku Pam wanda ya yi kaurin suna akan satar shanu a karamar hukumar Barikin Ladi.

Agundu ya kuma ce sun kama Isa Abdulladi, Usman Abdulkarim da Hassan Shu’aibu da zargin satar shanu, sannan wasu Musa Adamu, Ibrahim Musa da Alhassan Ahmed ana zargin su da hannu wajen kai hari a kauyen Kulben a kwanakin baya da ya kaiga asarar rayuka 12.

Rundunar Tsaron STF Ta Kama Masu Aikata Ta'addanci
Rundunar Tsaron STF Ta Kama Masu Aikata Ta'addanci

Sauran wadan da rundunar ke zargi da laifukan fashi da makami sun hada da Emmanuel Ebube, Tinchan Kumen, Solomon Dadong da wasu da aka kame laifin shiga kungiyar asiri suna cin zarafin al’umma.

Ya bayyana cewa an kama Umar Musa Tela da ake zargin dan dan Boko Haram ne wanda ya ce ya gudo ne daga garin Damagum a jihar Yobe sakamakon matsi na ‘Operation Lafiya Dole’.

Domin Karin bayani a saurari rahoton wakiliyar muryar Amurka Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG