Accessibility links

Rundunar 'yan sandan Afirka ta Kudu tace jami'anta sun bude wuta ne domin kare kansu


Wata mace tana kuka domin nuna bacin ranta da budewa ma'aikata wuta da 'yan sanda suka yi
Babbar jami’ar ‘yan sandan Afrika ta Kudu tace jami’anta sun bude wuta kan ma’aikatan hakar mu’adinai ne domin kare kansu, a wani tashin hankalin da yayi sanadin mutuwar mutane 34 wadansu 78 kuma suka ji raunuka.

Riah Phiyega ta bayyana yau jumma’a cewa, ‘yan sanda sun yi amfani da karfi ne domin kare kansu bayanda masu yajin aikin dake da miyagun makamai suka kai masu hari jiya alhamis. Kamfanin hakar mu’adinan ya kuma bayyana cewa, wadansu ma’aikatan dake yajin aiki sun dauki makamai bayan tashin hankalin.

Phiyega ta bayyana cewa, ‘yan sanda sun yi amfani da mesar ruwa da farko da kuma barkonon tsohuwa da nufin tarwatsa ma’aikatan, sai dai suka yi watsi da ‘yan sandan.
Babbar jami’ar ‘yan sandan ta kuma ce an kama kimanin mutane dari biyu da hamsin da tara dangane da aragangamar da aka yi a kamfanin hakar mu’adanan na Lonmin, dake tazarar kilomita dari da ishirin arewa maso yammacin birnin Johannesburg.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya katse ziyarar da ya kai Mozambique domin halartar taron kolun yankin.
XS
SM
MD
LG