Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'yan sandan jihar Osun ta damke wasu bata gari 26


Wasu masu fashi da makami da aka taba kamawa

'Yan sanda a jihar Osun sun samu nasarar kama masu aikata laifuffuka 26, ciki harda wanda yayi karyar cewa shi mace ce ta yanar gizo.

Runduanar ‘yan sandan jihar Osun, ta kama kuma ta gabatarwa taron yan jarida wadansu masu aikata laifuffuka 26 da suka harda da masu sata da garkuwa da mutane, da masu fashi da makami da wadanda suka kware wajen satar motoci da Babura da kuma wani wanda yayi shigar mata. Yace shi mace ce ta yanar gizo, har ya samu nasarar damfarar wani Ba’amerike batura dala dubu 80.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun Mr. Femi Oyeleye. Shi ya gabatarwa ‘yan jarida wadannan bata gari, a birnin Oshogbo baban birnin jihar Osun.

Yace wanda ya damfari Ba'ameriken ya gabatar da kansa a zaman mace ta yanar gizo, har ya samu nasarar dafarar baturen, daya sa masa kudin a asusu ajiyarsa na baki.

Kwamishinan yan sanda yace irin wannan zamba ke bata sunan Nigeria.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:02 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG