Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna Ta Yi Alkawarin Zakulo Wadanda Suka Kashe Jami’anta


Ibrahim Idris, babban sifeton 'yan sandan Nigeria,
Ibrahim Idris, babban sifeton 'yan sandan Nigeria,

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar cewa ‘yan bindiga sun kashe mata jami’ai hudu, ta kuma yi alkawarin farauto wadanda suka kashe su.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce kokarin da take yi na kwakulo wasu ‘yan bindiga ne ya sa aka kashe mata jami’anta guda hudu a lokacin da suka je yin wani aiki a unguwar Rigasa a garin Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar DSP Yakubu Sabo, wanda bai yadda wakilin Sashen Hausa ya dauki muryarsa ba, ya tabbatar cewa yanzu haka rundunarsu ta kara aikewa da karin jami’ai a wurin da ‘yan bindigan suka yiwa jami’an da suka kashe kwantan bauna. Sai dai har yanzu ba’a kama mutum ko daya cikin wadanda suka aikata wannan ta’annati ba.

DSP Sabo ya ce rundunar ta yi alkawari kama dukannin tsagerun dake tada kayar baya a jihar, walau barayin mutane ko kuma masu tada hayaniya a wasu bangarorin jihar.

Birgediya Muhammad Kabiru Galadanci mai murabus ya ce akwai lauje cikin nadi game da wannan batu. Yace kafin su tashi zuwa Jankasa kamata ya yi su aika da ‘yan sandan farin kaya da zasu taimaka wajen tara bayanai. Baicin hakan akwai ofishin ‘yan sanda a Rigasa kuma sun san wasu jami’an su na zuwa. Amma ayar tambaya nan ita ce yaya su ‘yan bindigan suka san za su zo, har suka yi masu kwantan bauna? A cikin jami’an tsaron akwai bara gurbi da yawa dake kewaya su tsguntawa miyagun mutanen duk abun da aka shirya za’a yi. Ya ce da jin labarin ya tabbata wani cikin ‘yan sandan ya bada labarin zuwan su saboda za’a bashi kudi dubu hamsin ko dubu dari.

Kwanakin baya, a wani kauyen dake kusa da Rigasa aka sace wani malamin addinin Musulunci Shaikh Ahmed Albarkawi wanda ya kwashe ‘yan kwanaki kafin barayin su sako shi.

A saurari rahoton Isa Lawal Ikara

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG