Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sanda A Jihar Taraba Ta Fara Aiwatar Da Dokar Kiwo.


Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta ce zata tabbatar an bi dokar hana kiwo barkatai.

A wani yanayi na ba sabam ba, rundunar 'yan sandan jihar Taraba tace zata tabbatar da aiwatar da wannan sabuwar dokar hana kiwon dake ci gaba da jawo cece-kuce a ciki da ma wajen jihar Taraba.

Wannan ma kuwa na zuwa ne yayin da wasu rahotanni ke cewa wasu jami’an tsaro tuni suka soma amfani da wannan dokar wajen tatsar makiyaya, walau a mota ko bisashe batun da kungiyoyin makiyaya ke cewa ba zata sabu ba.

To sai dai kuma rundunar 'yan sandan jihar ta bakin kakakinta, David Misal, ta ce zata sa ido wajen aiwatar da dokar kuma duk wanda aka kama yana karya dokar to fa labudda zasu kama shi.

To sai dai yayin da aka soma aiwatar da wannan doka, yanzu haka wasu kungiyoyin al’umma a jihar sun fara maida martani.

Barr. Muhammad Bello Mustapha na kungiyar ci gaban Taraba ta "Taraba Concern Citizen Forum" ya soki matakin soma aiwatar da dokar a wannan lokaci da kasar ke fama da tashe-tashen hankula dake da nasaba da rikicin makiyaya da manoma.

Ga Ibrahim Abdulazeez da Karin bayani 4’15

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG