Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'Yansandan Abia Ta Ceto Yara Da Aka Sato Daga Jihar Delta


Wasu da suka sace mutum
Wasu da suka sace mutum

Sace mutane a Najeriya na neman ya zama ruwan dare gama gari domin a Abia rundunar 'yansandan jihar ta ceto wasu yara biyu da aka sato daga jihar Delta akan hanyarsu ta zuwa kasuwar sayarda su.

Rundunar 'yansandan jihar Abia ta samu nasarar ceto wasu yara guda biyu da aka sato daga jihar Delta da nufin sayarda su a jihar Akwa Ibom.

Rundunar tace tayi anfani da wasu bayanan siri wajen cetosu. Rundunar ta kuma kama wasu da ake zarginsu da sato yaran.Kwamishanan 'yansandan Abia Adamu Ibrahim Kanoma ya tabbatar da aukuwar lamarin. Yace idan sun sato yaran wasu 'yansanda sukan tsaya a matsayin masu son su sayi yaran ta hakan sai a kamasu. Ta haka suka kama wadanda suka sato yaran daga Delta.Sun kama wadanda suka sato yaran da wadanda suka sayarwa duk suna hannun 'yansanda.

Kwamishanan yace ya zagaya al'ummomin jihar domin neman hadin kansu dangane da sace mutane da kuma nuna bata gari dake fakewa cikinsu suna aikata miyagun laifuka. Sun ba alummomin lambobin 'yansanda da zasu iya kira su basu labari cikin siri ba tare da bayyana kansu ba da zai taimaka wurin gano bata gari kafin su aikata barna. Yace harkar tsaro yanzu harka ce da ta shafi kowa da kowa.

Al'ummomin jihar ta Abia sun yi na'am da kiran kwamishanan kuma sun ce a shirye suke su bada hadin kai. Zasu bada duk wani labari da zai taimaka musamman ganin yadda kasar take.

Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG