Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda A Nijar Sun Kama Kwayoyi Daga Najeriya


Kwayoyin Tramol da aka kama da suka shigo daga Najeriya

Rundunar 'yan sandan Nijar ta kama kwayar da aka shigo da ita daga tarayyar Najeriya a birnin Konni, birnin dake makwaftaka da kasar wanda tazarar kilomita biyar ne kawai ya raba su.

Kwayar tramol din da aka kama ta kai dubu dari da hamsin wadda take sa mutum ya fita daga cikin hayyacinsa.

Malam Hashimmu Shuda wanda ya kasance kwamishanan 'yansandan birnin Konni yayi karin bayani dangane da kamen..

Birnin Konni yana iyaka da tarayyar Najeriya kuma yana tsakiyar Jamhuriyar Nijar ya sa masu shigowa da kwayar kan jaraba bin ta birnin mafi yawancin lokaci domin isa arewacin Nijar da zummar ketarewa zuwa kasashen turai.

Bayan kamun gwamnan jihar Tawa Malam Musa Abdulrahaman ya je birnin Konni domin gani da idanunsa musamman ganin cewa kwayar nada dimbin yawa.

Malam Audu Alhaji Mamidu magatakardan ofishin gundumar Konni yayi karin bayani game da irin jinjinawa da suke yiwa jami'an tsaro. Yana mai cewa kamun ba shi ba ne farko. Ya karfafa jami'an tsaron da su kara kaimi su cigaba saboda birnin Konni tamkar mararraba ce tare da cewa duk inda za'a tafi ta birnin ake bi.

Kasancewa shan kwaya na cikin abubuwan dake tunzura mutane yin miyagun ayyuka, musamman matasa, shi ya sa kwamishanan 'yansanda yayiwa mutane da matasa nasiha ganin cewa tazarar kilomita biyar ne kawai yake tsakanin Najeriya da Konni.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG