Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar sojan Nigeria ta lalata sansanonin yan Boko Haram


Sojoji Najeriya kusa da Maiduguri.

Rundunar sojan Nigeria, shiya ta bakwai dake birnin Maiduguri, arewa maso gabashin Nigeria ta samu nasarar lalata sansanonin yan Boko Haram a karamar hukumar Konduga

Rundunar sojan Nigeria shiya ta bakwai dake birnin Maiduguri arewa maso gabashin Nigeria, ta kai hari akan yan Boko Haram a kauyukan Kushembiri da Walmure a karamar hukumar Konduga.

Mataimakin direktan hulda da jama' na rundunar, Kanal Tukur Gusau ya shedawa maneman labaru cewa sun shiga wadannan kauyukan ne inda suka fafata da yan Boko Haram, harma suka samu nasarar kashe wasu da dama.

Haka kuma yace sun samu nasarar kubutar da mutane 57 da suka hada da yara da mata da kuma dattijai. Kanal Gusau yace yan Boko Haram sunyi garkuwa ne da mutane. To amma kuma yace ba'a kama dan tawaye ko daya ba..

Kanal Gusau yace sojoji sun samu mota kirar Land Rover da Tifa wadanda ake amfani dasu domin aikin ta'adanci.

Cikin wadanda aka kubutar akwai yara 25, da mata 29 da kuma datijjai guda 5. Yace tuni rundunar soja ta lata tungayen yan Boko Haram. Yace illahirin kauyukan an kewaye su da tutocin yan Boko Haram.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

XS
SM
MD
LG