Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwa Da Muhalli Masu Tsabta Suna Da Muhimmanci A Rayuwar Kananan Yara


Yara suna wasa
Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa, samar da ruwa da muhalli masu tsabta suna da muhimmanci wajen kare lafiya da rayukan kananan yara.

Bisa ga cewar asusun UNICEF, dole cibiyoyi da masu ruwa da tsaki su kara kokari a wannan fannin idan ana son cimma nasarar rage yawan mace macen kananan yara.
Asusun ya bayyana cewa rabin adadin kananan yara kasa da shekaru biyar da suke mutuwa a duniya daga Najeriya suke. Cibiyar UNICEF tace yara da yawa suna mutuwa ta dalilin kamuwa da zawo wanda aka fi samu tsakanin kananan yaran da suke zama a gidaje marasa tsabta ko shan ruwa marar tsabta.

Bisa ga binciken asusun UNICEF yaran da suke zaune a yankunan karkara sun fi kamuwa da zawo sakamakon rashin yanayi da ruwa mai tsabta.
Akwai mutane miliyan 66 da basu da ruwa mai tsabta a Najeriya daga cikin miliyan 783 da suke fama da rashin ruwa a duniya baki daya.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG