Korea ta Arewa ta ce, Shugaba Kim Jong Un ya jagoranci wani sabon gwajin makamin roka, wanda rahotanni suka nuna cewa, zai kara damar iya kai hari a Korea ta kudu, har da ma sansanin sojin Amurka da ke yankin.
A yau Asabar, kamfanin dillancin labaran kasar ta Korea ta Arewa, ya ruwaito cewa, shugaba Kim ne ya jagoranci gwajin wannan sabon mamaki na roka.
Rahotan na zuwa ne kwana guda bayan da gamayyar hafsan hafsoshin sojin Korea ta Kudu ta ce makwabciyarta ta Arewa, ta harba wasu makamai makamancin wannan guda biyu da misalin karfe 3 na safe agogon yankin, daga Lardin da ke kudancin Hamgyong.
Makaman a cewar hukumomin na Korea ta Kudu, sun yi tafiyar kilomita 220, wanda wannan ya kawo adadin makaman da ta gwada zuwa uku cikin dan sama da mako guda.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kore duk wata da ake nunawa kan wadannan gwaje-gwaje.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 18, 2023
Mataimakin Shugaban Gambia, Badara Alieu Joof Ya Rasu A India