Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Kakakin ISIS Ya Kira 'Yan Kungiyar Su Farma Makiyansu Koina A Duniya


Mayakan ISIS

Sabon kakakin kungiyar ISIS da aka nada yana kira akan magoya bayan kungiyar a ko ina suke a duniya da cewa su tasarwa makiyan kungiyar, suyi ta fattakarsu har, kamar yadda yace, sai “sun kona wutar dake karkashin kafafunsu.”

A cikin wani faifan da sashenta watsa labarai na al-Furqan ya sako ne, ISIS ta bada sanarwar nada Abu hassan al-Muhajir sabon kakakinta don ya maye gurbin Abu Muhammad al-Adnani wanda wani harin Amurka ya hallaka shi a kusa da garin al-Bab na kasar Syria a cikin watan Agustar da ya wuce.

A cikin faifan ne aka ji al-Muhajir yan kira ga magoya bayansu da cewa su kadarwa makiyan nasu a ko ina suka same su, kama da kasuwanni, kan hanya, a cikin gidajen holewa da ma duk sauran wurare.

Haka kuma, a cikin jawabin da ya wa lakabi “Zaku tuna abinda na gaya muku”, al-Muhajir yayi alkawarin cewa kungiyar tasu zata kai sababbin hare-hare akan kasashen Amurka, Rasha, Tura,i Iran da kuma Turkiyya, wacce daga cikin dukkan kasashen, itace ya fi caccaka sosai.

XS
SM
MD
LG