Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Rikici Ya Barke a Kasar Afirka ta Tsakiya


Shugabar gwamnatin rikon kwarya ta Afirka ta Tsakiya Catherine Samba-Panza da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon

Wani sabon rikicin da ya sake barkewa tsakanin kiristoci ta musulman kasar Afirka ta Tsakiya ya tilastawa shugabar gwamnatin rikon kwarya barin taron Majalisar Dinkin Duniya da yanzu ake yi a New York bazata

Shugabar rikon kwaryar Jamhuriyar Africa ta Tsakiya Catherine Samba-Panza ta bar taron shugabannin duniya na Majalisar Dinkin Duniya da ake yi anan Amurka ba shiri don komawa gida a dalilin sabon rikicin da ya barke a babban birnin kasar.

Rahotanni daga birnin Bangui na nuna cewa, an kashe mutane da dama a rikicin da ya barke tsakanin Kirista da Musulmi sakamakon mutuwar wani Musulmi. Haka ma wasu fursunoni sun tsere daga gidan yari.

Mutane 3 kuma sun mutu sakamakon taruwa a tsakiyar birnin don yin zanga-zanga zuwa fadar shugaban kasar. Masu zanga-zangar sun dora alhakin mutuwar mutanen a kan rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya da suka ce sun yi harbi cikin jama’a.

Tuni dai rundunar wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya ta musanta wannan zargi. Amurka ta yi tir da rikicin sannan ta yi alkawarin taimakawa kasar ta Afirka ta Tsakiya.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG