Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Sakataren OPEC Ya Bukaci Kasashen Kungiyar Su Yi Taron Gaggawa


Tutar OPEC a jikin ginin hedkwatarta

Faduwar darajar man fetur na ci gaba da haddasa koma baya ga kasashen da suka dogara dashi,batun da sabon babban sakatare Janar na kungiyar OPEC ta kasashe masu arzikin man fetur a duniya,Muhammad Sanusi Barkindo.

Sabon sakataren ya bukaci da a gudanar da wani taron gaggawa na kasashen mambobin kungiyar domin tattaunawa kan yadda farashin man ke kara faduwa.

A cikin kwanakin nan ne ma kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya, wato, OPEC, ta sanar da Mohammed Barkindo daga Najeriya a matsayin sabon Sakatare Janar na kungiyar.

Barkindo, wanda ya maye gurbin Abdalla El-Badri dan kasar Libya , wanda ke rike da mukamin tun shekarar 2007,yace dole kasashe su tashi tsaye

Shugaban kungiyar ya fada a wani ganawa da yayi da manema labarai a filin saukan jiragen sama na kasa da kasa dake Yola. Yace akwai bukatar karatun ta natsu game da yadda darajar mai dama iskar gas,ke kara faduwa a kasuwannin duniya.

Shugaban kungiyar ta OPEC, yace ‘’ Wannan al'amari dai ya zo ne a daidai lokacin da farashin man fetur ke ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya. Kuma dole a tashi tsaye don fuskantar kalubalen dake akwai.

‘’Da farko ma dai dole mu daura damara ta hanyar samun hadin kai da fahimtar juna a tsakanin membobin kungiyar ta OPEC,don tinkaran wadannan matsaloli ba wai kawai ga OPEC ba,kai harma da fannin man fetur da kuma iskar gas.

‘’Kuma na san kasata Najeriya zata yi duk abun da ya kamata ta ga an samu wakilci na gari,’’ a cewarsa.

To sai dai kuma daa juya ga hare haren yankin Neja –Delta, sabon Sakatare Janar din,ya nuna kaduwarsa game da abubuwan dake faruwa,da yace hakan na jawo wa Najeriya babbar asara.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG