Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Gwamnatin Hungary Zata Kafa Dokar Hana Tallafawa 'Yan Ci Rani


Firayim Ministan Hungary, Viktor Orban mai kyamar 'yan cirani ko bakin haure

Kwana daya da lashe zaben kasa jam'iyyar dake mulkin Hungary zata nemi kafa dokar da zata hana kungiyoyin fararen hula tallafawa 'yan ci rani

Kwana daya bayan da Firayim Ministar kasar Hungary Viktor Orban ya sami gagarumar nasara a zaben kasar, karkashin yakin neman zabe da yake kyamar baki, jam'iyyar dake mulkin kasar tace zata nemi a kafa dokokin da zasu hana kungiyoyin farar hula tallafawa 'yan ci rani.

Jami'an jam'iyyardake mulkin kasar da ake kira Fidesz sun ce majalisar dokokin kasar zata fara aiki kan dokoki da za su hana masu rajin kare bakin haure da 'yan ci rani da zarar ta koma bakin aiki a farkon watan Mayu mai zuwa.

Daftarin dokar zata tilastawa kungiyoyin dake taimakawa 'yan ci raninsu sami izini ministocin harkokin cikin gida na kasar su gudanar da aikin su, kana gwamnati zata aza harajin kashi 25 cikin dari kan gudumawar da irin wadannan kungiyoyi suke samu daga kasashen waje.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG