Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Wakar Namenj, Hamisu Breaker Na Haskawa


Namenj, hagu da Hamisu Breaker, dama (Hoto: Namenj Shafin Instagram)

Sabuwar wakar Namenj mai taken “Da ma” tana ci gaba da haskawa da jan hankulan masoyan wakokin zamani na Hausa musamman a shafukan sada zumunta.

Wakar, wacce ya gayyaci mawaki Hamisu Breaker don ya taya shi rerawa, an sake ta ne akan shafin Youtube a makon da ya gabata, kuma tuni har yawan wadanda suka kalla ya haura mutun dubu 100.

Ga kadan daga cikin wasu baitukan wakar:

Baby ina Kwana?

Baby ina gajiya?

Shin kin tashi lafiya……?

Tabbas kin iya soyayya

Da ma da ke na fara haduwa,

Da na yi aure tuntuni

Zama da ke akwai karuwa…..

Namenj (Hoto: Shafin Instagram Namenj)
Namenj (Hoto: Shafin Instagram Namenj)

Namenj wanda a baya ya yi wakar “Fatana” wacce ya saka a watan da ya gabata, ya fito idon duniya ne bayan da ya dauki salon kwaikwayon wakokin fitattun mawaka har da na kudancin Najeriya da ma na kasashen waje.

Ya maimaita wakokin fitattun mawaka kamar Ali Jita da wasu wakokin da aka yi a wasu fina-finan Hausa.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG