Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Yarjajjeniya zai Sassauta Tashin Hankali a Ukraine


ukraine-nato
ukraine-nato

Babban kwamandan NATO ya ce ya na da karfin gwiwar cewa sabuwar yarjajjeniyar nan ta ware wani gandun da ba a harkar soji ciki tsakanin sojojin gwamnatin Ukraine da 'yan aware masu ra'ayin Rasha, zai sassauta tashin hankalin.

To amma Janar Philip Breedlove na sojojin saman AMurka, ya ce halin da ake ciki yanzu ba mai kyau ba ne, saboda sojojin Rasha na cikin Ukraine.

Breedlove ya ce yarjajjeniyar tsagaita wutar da aka cimma a farkon wannan watan na jeka-na-yika ne kawai, ganin yadda tashe tashen hankula a cikin 'yan kwanakin da su ka gabata, su ka kai yadda su ke gabanin yarjajjeniyar.

Karkashin wannan sabuwar yarjajjeniyar da aka cimma a birnin Minsk a jiya Asabar, da sojojin Ukraine da dakarun 'yan aware, dole ne su janye bindigogin atilarensu baya, da tsawon kilomita 15 daga inda kowannensu ya ja daga, don a samu gandu mai fadin kilomita 30 murabba'i.

Yarjajjeniyar, wadda ake wa lakabi da "Yarjajjeniyar Minsk" ta kuma bukaci kowani sashi ya janye dukkan sojojin haya na kasashen waje daga inda ake rigimar a gabashin Ukraine. Rasha ta musanta zargin Ukraine da kasashen Yammacin Duniya cewa sojojin Rashar su kan je yaki da 'yan tawayen.

To amma, Breedlove ya ce sojojin Rasha na gabashin Ukraine, kodayake yawansu ya ragu.

XS
SM
MD
LG