Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasarmu Ta Bambanta Da Ta Yankin Su Goodluck Jonathan


Shugaban Kasa GoodLuck Jonathan

A wani martani ga shugaba Goodluck Jonathan da yayi ikirarin cewa 'yan PDP da suka canja sheka zasu gaji su koma da yunwa, Sa'idu Adamu yace siyasar Arewa ta akida ce ba kudi ko mukami ba.

Tsohon dan majalisar jihar Kaduna, kuma tsohon kwamishinan yada labarai na Jihar, Malam Sa'idu Adamu, ya bayyana cewa siyasar Arewa ba irinta kudancin Najeriya ba ce.

Da yake mayar da martani ga kalamun shugaba Goodluck Jonathan ga 'yan jam'iyyar PDP da suka canja sheka zuwa APC cewa zasu komo da yunwa, Malam Sa'idu Adamu ya kare canja shekar da shi da wasu kusoshin PDP suka yi tare da bayyana dalilansu na barin jam'iyyar PDP wadda ta sha kaye a babban zaben da aka gudanar kwanakin baya.

“Siyasa ta mu ta ‘yan Arewa ta sha ban ban da irin siyasar su ta ‘yan kudu maso kudancin Najeriya, su suna siyasar kudi ko mukami ne kawai mu kuma muna yi ne domin akida, da kuma mutumci. Bamu dauki siyasa a sana’ar da zamu ci abinci da ita ba, tun kafin siyasar bamu rasa abin da zamu ci ba.”

Daga karshe yayi Karin bayanin cewar duk wanda yake siyasa domin jama’a to dole ne ya taimaki kanshi ya koma inda zaiyi tafiya tare da sauran jama’a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:05 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG