Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakatare Rex Tillerson Ya Gana Da Minista Sergei Lavrov A Moscow


Jami'an Diplomasiyyar guda biyu sun yarda cewa ganawar ta su na zuwane a lokaci mai muhimmanci saboda dangantakar dake tsakanin kasashensu.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fada yau Laraba cewa gwamnatin kasarsa ta sha samun tambayoyi dangane da matakai marasa kan-gado kuma cike da rudani da sabuwar gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump take dauka.

Lavrov yana maganar ne a wajen taron da suka fara da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson a Moscow, ya kara da cewa akwai bukatar Rasha ta fahimci manufar Amurka.

Lavrov kuma ya ambaci farmakin da Amurka ta kai Siriyya a makon da ya gabata, wanda maida murtani ne ga harin gubar da aka kai a Siriyya din, ya bayyana murtanin da Amurka ta maida a matsayin “abun damuwa”.

Tillerson bai yi wata doguwar magana a nasa jawabin ba, amma kamar Lavrov, shima ya ce ganawar ta yau Laraba na zuwane a lokaci mai muhimmanci kuma zata basu damar yin cikakkiyar tattaunawa akan bambamnce-bambancensu da kuma muradansu.

Facebook Forum

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG