Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Kerry Zai isa Kasar Izra'ila Yau Akan Falasdin


John Kerry da Natanyahu

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai isa kasar Isira'ila a yau domin tattaunawar diflomasiyyar zaman lafiya da Falasdinawa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry zai isa kasar Isira'ila a yau dinnan Litini, a yinkurin wannan babban jami'in diflomasiyyar Amurka na ceto tattaunawar zaman lafiya da Falasdinawa daga jicewa.

Kerry zai kai ziyara ta biyu cikin kasa da mako guda kenan zuwa wannan yankin. Makon jiya ya je Jordan don tattaunawa da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas.

Fafatukar samar da zaman lafiyar ta gamu da takaddama sosai cikin 'yan kwanakin nan, yayin da Isira'ila ta ki yadda ta saki rukuni na karshe na Falasdinawan da ke fursuna kamar yadda aka yi yarjajjeniya.

Sakin Falasdinawan wani bangare ne na yarjajjeniyar da ta kai ga dawo da bangarorin biyu bisa teburin shawara har na tsawon watanni 9, daga watan Yulin da ya gabata.

Isira'ila ta ce ta na so a tsawaita tattaunawar gaba da wa'adi mai karewa a watan gobe, kafin sakin fursunonin. Amma Falasdinawa sun ki, su ka ce za su kaurace ma tattaunawar daga yanzu muddun Isira'ila ta ki sakin fursunonin kamar yadda aka tsaida.
XS
SM
MD
LG