Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Dora Alhakin Halin da Yan Kabilar Rohingya Ke Ci Kan Shugabannin Sojojin Myanmar


Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen Amurka

A jiya Laraba, sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya fadi cewa yana daura laifin dukkan tashe-tashen hakalin dake faruwa a Myanmar kan shugabannin sojan kasar.

‘Yan kabilar Rohingya sama da rabin miliyan suka tsallaka iyaka zuwa kasar Bangladesh dake makwabtaka da Myanmar a ‘yan makonnin nan, mutanen dai na gujewa gallazawar da sojojin Burma ke yi, bayan da ‘yan tawayen Rohingya suka kaiwa jami’an tsaron kasar hari.

Fattakar da ake yiwa ‘yan Rohingya, wadda ta yi sanadiyar kisan kare ‘dangi, ta janyo suka da Allah wadai daga kasashen duniya, duk da yake har ya zuwa yanzu hukumomin Myanmar na ci gaba da musunta tashin hankalin da ke faruwa a kasar.

Jawabin sakatare Tillerson na zuwa ne bayan wani rahoton kungiyar kare ‘yancin bil Adama ta Amnesty International, wanda cikinsa take zargin jami’an tsaron Myanmar da cin zarafin ‘yan kabilar Rohingya.

Rahotan, wanda aka hada shi ta hanyar yiwa ‘yan gudun hira 100 tambayoyi, na cewa jami’an tsaron sun harbe daruruwan ‘yan Rohingya dake kokarin guduwa daga kauyukansu, suka kuma kone tsofaffi da marasa lafiyan da ba zasu iya guduwa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG