Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya zai kai ziyara Nigeria

Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon
Baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon

Ranar Lahadi idan Allah ya kaimu aka shirya, baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon zai kai ziyara Nigeria domin ganawa da sabon shugaban kasar Muhammdu Buhari da kuma tunawa da mumunar harin da aka kaiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja a shekara ta dubu biyu da goma sha daya.

Jiya Juma'a jami'an Majalisar Dinkin Duniya suka ce Mr Ban zai gana da shugaba Muhammadu Buhari wanda ya dare kan ragamar mulki a watan Mayu. Haka kuma Mr Ban zai gana da wasu jami'an gwamnatin da wakilan kungiyoyin jama'a da kuma yan kasuwa.

Mai magana da yawur Majalisar Dinkin Duniya Eri Kaneko ta kuma ce, a yayin ziyarar, ana sa ran Mr Ban zai tattauna batutuwan raya kasa da canjin yanayi da kare hakki da yanci jama'a da kuma yadda za'a dakile mumunar ra'ayin rikau.

Haka kuma baban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya zai yi bikin tunawa da mununar harin kunar bakin waken da aka kiwa ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Abuja a shekara ta dubu biyu da goma sha daya daya kashe mutane ashirin da daya.

Daga Nigeria Mr Ban zai wuce zuwa birnin Paris kasar Farasa domin tattauna shirye shirye baban taro da za'a yi akan canjin yanayi a watan Disamba idan Allah ya kaimu. Zai kuma gana da shugaban Faransa Francoise Hollande.

XS
SM
MD
LG