Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Tsaron Amurka Ya Ce NATO Zata Shawo Kan Rasha Ta Amince da Dakile Yaduwar Makamai


Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis

Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis, ya ce ministocin tsaron kungiyar Tsaro ta NATO, na duba hanyoyin da za su janyo Rasha ta rika nuna ladabi ta hanyar amfani da wata yarejejeniyar dakile yaduwar makamai.

Yayin wani jawabi da ya yiwa manema labarai a hedkwatar NATO da ke Belgium, Mattis ya ce, yunkurin dawo da Rasha kan layi bisa wannan yarjejeniya da ta sa hannu, na da muhimmanci.

Ita dai Amurka ta dage cewa Rasha na fitar da makamai masu linzami wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar, wacce ake wa lakabi da INF a takaiace.

Wannan yarjejeniya dai ta haramta fitar da makaman nukiliya masu linzami, wadanda ke tafiyar matsakaicin zango akan doron kasa.

Rasha a nata bangaren, ta sha musanta wannan zargi da ake cewa ya sabawa yarjejeniyar ta INF, sannan ita ma ta zargi Amurka da sabawa wannan shiri.

Hukumomin Moscow sun yi zargin cewa za a iya kai musu hari da makamai masu linzamin da Amurka ta girke a Poland da Romania idan aka inganta musu fasali.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG