Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren tsaron Amurka yace Amurka tana son a magance zaman tankiya da Korea ta arewa cikin lumana


Sakataren tsaron Amurka Jim Mattis

Sakataren tsaron Amirka Jim Mattis ya jaddada cewa Amirka tana son a magance zaman tankiya da Korea ta arewa dake kara yin kamari cikin lumana.

Talata sakataren tsaron Amirka Jim Mattis ya jaddada cewa Amirka tana son a magance zaman tankiya da Korea ta arewa dake kara yin kamari cikin lumana.

Jim Mattis yayi wannan furucin ne duk da cewa kasar Korea ta arewa tayi ikirarin cewa furucin da shugaban Amirka Donald Trump yayi ta dandalin tweeter jiya Litinin, tamkar ayyana yaki ne akan kasar.

Sakataren tsaron na Amirka wanda a halin yanzu yake ziyara a birnin New Delhi na kasar Indiya domin tattaunawa da jami’an kasar akan karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Yace a yayinda kasancewar sojojin Amirka a zirin Korea ya zama wajibi domin tinkarar barazanar Korea ta arewa, Amirka tana goyon bayan yunkurin diplomasiya na magance wannan rikici cikin lumana.

Yace burinsu ke nan, kuma yayi Imani, shi kansa shugaba Donald Trump ya fito filli ya baiyana wannan matsayi akan wannan batu. Mr Mattis yayi wannan furucin ne bayan ya gana da Ministan tsaron kasar Indiya.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG