Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sallar Idi a Kano

Imam Shiek Abubakar Jibril ya hori al’ummar musulmi a yau dinnan dasu hada kansu su kwaunaci juna kuma suyiwa junansu afuwa, ya kara magan akan muhimmancin layya ga rayuwar musulmi, Inda yace idan zakayi yanka da duk ibadar dazakayi kayi saboda Allah, kuma zakaji mutane dama nacewa inbadan yaran nan ba ko saboda yarannan bari inje in sayo ko kaza ne, to ai kaga saboda yaran yayi yanka bashida ladan yanka saboda badan yayi ba Allah ba. Kayi yanka kamar yadda Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace kamar yadda Allah yace. Mallam dai yayi huduba mai taba zuciya kuma yakamata musulmi su dauka suyi amfani da ita kuma Allah yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Sai kuma mai martaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sunusi na biyu yayi hawan sallah na farko tun bayan hawansa karagar mulki, a inda yayi jawabi ga al’uma inda yayi bayani akan wannan shekara damuke ciki, kashe kashe da kone kone sunyi yawa ga mutane wanda ya nuna wa’yannan abune marasa dadi kuma shari’ar addinin musulunci bai yarda dasuba, kuma ya roki jama’a dasu zama dogaran doka duk in da akaji ko aka ga irin wanna ‘bata gari da a gaggauta sanar da hukuma mafi kusa domin a dauki matakan dasuka kamata wajen dakilesu. Yakuma roki mutane dasu yawanta yin addu’a domin neman magani ga duk annoba kamar cutar Ebola, yakara tunatar da jama’a wajen kula da illimin yara da mata dakuma kiyaye darajar aure.

Sallar Idi A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG