Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanadiyar Yawan Ruwan Sama a Nijar Zazzabin Cizon Sauro Na Yaduwa


Ambaliyar ruwan sama da ya haddasa yawan sauro dake kara zazzabin cizon sauron

Ruwan sama da ake tayi a Nijar ya sa zazzabin cizon sauro karuwa inda kawo yanzu mutane130,000 suka kamu kuma tuni 140 suka rasu

Sanadiyar ruwan sama da ake samu da yawa zazzabin cizon sauro yanzu ya fara addabar jama'a.

Marasa lafiya sun bayyana yadda cizon sauro ya jawo masu rashin lafiya musamman yara. Marasa lafiyan tare da 'ya'yansu da suka kamu sun nufi asibiti domin karbar allura.

Dr Habu Yahaya daraktan hukumar kiwon lafiya ta jihar Damagaran ya bayyana matsayin cutar. Yana mai cewa kawo yanzu 130,000 ne suka kamu da cutar a jihar Damagaran tun farawar wannan shekarar. Kawo yanzu 141 ne kuma suka rasu.

Hajiya Yahaya ita ma jami'ar kiwon lafiya dake kula da mata masu juna biyu da yara tace an samu cigaba sanadiyar yin la'akari da matakai da kuma bin gargadin likitoci. Bugu da kari mahukumta na bi suna rabawa iyaye magani na yara tun daga haihuwa har yaro ya kai shekaru biyar. Haka ma mata masu juna biyu ana basu rigakafi. Ana kuma raba gidan sauro mai magani.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG