Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanatoci Na Goyon Bayan Kwato Kudaden Yakar Boko Haram Da Buhari Ke Yi


Shugaba Muhammadu Buhari

Yayin da yaki da mahandaman kudaden tabbatar da tsaron Najeriya ke kara zafafa, 'yan Majalisar Tarayyar Najeriya sun bayyana aniyarsu ta goyon bayan Shugaban a cewar wani shugaban kwamiti.

Yayin da gwamnatin Najeriya Najeriya ke cigaba da zafafa kokarin kwato kudaden da aka ware a baya don yaki da ‘yan Boko Haram daga wajen wadanda ake zargin sun handame, Majalisar Dattawan kasar ta ce ta na goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari, kan matakin da ya ke daukawa na farauto kudaden saboda a dakile Boko Haram da sauran matsalolin tsaro don talaka ya samu ya dan sarara.

Shugaban Kwamitin Ayyukan Musamman Na Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Abdul’aziz Murtala Nyako ne ya tabbatar ma menema labarai hakan a Yola, hedikwatar jahar.

To saidai kuma ba a taru aka zama day aba, saboda akwai kuma masu caccakar matakan da ake daukawa na kwato kudaden daga wadanda ake zargin sun wawuren.

Ga dai wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:14 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG