Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanatocin dake goyon bayan Bukola Saraki sun lashi takobin kareshi


Dr Bukola Saraki kakakin majalisar dattawan Najeriya

'Yan majalisar dattawa da dama dake mara wa shugaban majalisar baya Dr. Bukola Saraki sun lashi takobin kare shugaban daga masu kiran ko a tsigeshi ko ya yi murabus

Shugaban majalisar Dr Bukola Saraki na fuskantar tuhuma a kotun kula da da'ar ma'aikata dangane da rashin bayyana kaddarorinsa yayinda ya tsaya takarar neman gwamnan jihar Kwara shekaru goma sha uku da suka wuce.

Sanata Ibrahim Gobir daga jihar Sokoto yana cikin wadanda suka raka Dr Saraki kotu a zamanta na biyu. Yace ba wani abu ba ne kokari ake yi a jawo masa matsala. Batutuwan da suka kawo suna da ban dariya. Yace yaushe cin bashi ya zama haram? Ana dai son a cutar da shi ne.

Batun tsige Saraki daga mukaminsa abu ne mai kaman wuya domin sai an samu amincewar biyu bisa uku na 'yan majalisar. Babu tabbacin samun hakan

Sanata Isa Hamma Misau yace basu da wannan hadin kan domin jam'iyyar bata da gaskiya. Bata yiwa Saraki adalci. Suna nuna masa kiyayya. Me ya sa basu sa Faleke gaba ba wanda yaki ya je ya zama mataimakin gwamnan jihar Kogi. Ya fito kafar talibijan ya yi kacakaca da shugabancin jam'iyyar kuma basu yi masa komi ba. Basu sa Faleke gaba ba domin yana da ubangida ba kamar Saraki ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG