Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanyi Zai Halaka 'Yan Gudun Hijira Da Bakin Haure A Turai.


Sasanin da wasu 'yan gudun hijira suke a Girka.
Sasanin da wasu 'yan gudun hijira suke a Girka.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya Ne Suka Yi Wannan Kashedin bayan rahotanni masu tada hankali da suka samu.

Hukumomin agaji na Majalisar Dinkin Duniya suna gargadin cewa dubban 'yan gudun hijira, da bakin haure ko 'yan ci-rani, wadanda suke Girka da kasashe da suke yankin Balkans, wadnada suka gudo daga Syria, da Iraqi, da Afghanistan, da Afirka, da wasu wurare daban daban suna fuskantar kasadar mutuwa sakamkon matsanancin sanyi da ya lullube turai.

Hukumomin sun roki hukumomin turai da su gaggauta taimakawa wadanda mutane da suka tagayyara ta wajen sama musu muhallai da wasu muhimman bukatu domin su rayu cikin watanni masu zuwa.

Hukumomi kamar mai kula da 'yan gudun hijira da asusun tallafawa yara da ake kira UNICEF, suna tallafawa 'yan gudun hijiran da bakin haure wadanda suka makale a Girka da kuma yankin Balkans.

Duk da haka sun amince duk irin kokarin da suke yi, kokarinsu bai wadatar ba,saboda haka tilas ne gwamnatoci a fadin Turai su kara tallafawa, kodashike bakin haure da suke isa turai ya ragu sosai cikin watan nan.

Kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Cecile Pouilly, tace hukumar ta sami rahotanni masu tada hankali kan mace macen 'yan gudun hijira da bakin haure yayinda suke tafiye tafiye a fadin turai.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG