Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarakunan Hausawa, Igbo Da Yoruba Sun Gana A Lagos


Wasu mata suna sayen kaya a kasuwar gwanjo ta Katangua dake Lagos.
Wasu mata suna sayen kaya a kasuwar gwanjo ta Katangua dake Lagos.

Sarakunan manyan kabilun uku a yankin kudu maso yamma sun ce su na bukatar tabbatar da ci gaba, tare da bunkasar hadin kai da fahimtar juna.

Sarakunan manyan kabilu uku na Najeriya dake yankin kudu maso yammacin kasar, sun yi taron koli a Lagos, cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Najeriya, inda suka sake jaddada matsayinsu na cewa Najeriya dai kasa daya ce, kuma tilas dukkan jama'a su koyi zama tare da juna.

Sarakunan na Hausawa da Igbo da kuma Yoruba, sun kuma jaddada hadin kansu tare da yin kira ga jama'a da su guji nuna bambancin kabila, su rika mutunta juna domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali bda kuma ci gaba a duk fadin kasa.

Sarakunan sun bayyana takaicin irin abubuwan da suke faruwa a yankin arewacin Najeriya tare da bayyana kudurinsu na tabbatar da cewa irin wannan fitina ba ta shigo yankin kudu maso yammaci ba.

Wakilin Sashen Hausa, Ladan Ibrahim Ayawa, ya halarci zaman taron sarakunan, daga inda ya aiko da wannan rahoto.

Sarakunan Hausawa, Igbo da Yoruba A Kudu Maso Yamma Sun Yi Babban Taro A Lagos - 3:14
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG